11 Janairu 2021 - 11:00
Iran Da Cuba Za Su Yi Hadin Guiwa Game Da Rigakafin Covid-19

Kasashen Iran da Cuba, sun amince yin aiki a shirin samar da rigakafin cutar korona.

ABNA24 : Bangarorin biyu sun cimma matsaya wajen gwaji da kuma samar da rigakafin cutar ta Covid-19.

A ranar Juma’a data gabata dai jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa kasar ba zata karbi riga kafin korona ba wanda kasashen Amurka da Biritaniya suka samar, saboda kasashen ba abun yarda ne ba.

Iran dai na mai fatan fara sarrafa rigakafin data samar na cutar ta korona na da watanni biyu masu, idan gwajin da ake kansa ya bayar da sakamako mai kyau.

342/